ABNA24 : A wani martaninta ga kalaman Shugaba Joe Biden a kan gwaje-gwajen manyan makamai, Koriya ta Arewa ta yi barazanar sake gwaje-gwajen nata, wani matakin tamna tsakuwa na farko da kasar ke yi tun bayan zuwan sabuwar gwamnati a Amurka.
A ranar Alhamis da ta gabata ne dai kasar ta harba wasu makamai biyu daga gabashin gabar tekun Japan, abin kuma da Shugaba Joe Biden ya ce ya saba wa yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya.
Hakan kuma ya biyo wani atisayin hadin gwiwa ne tsakanin sojojin Amurka da na Koriya ta Kudu, lokacin wata ziyarar da Sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken da na tsaro Lloyd Austin a yankin.
342/